ME AKE NUFI DA CRYPTOCURRENCY
Assalamu Alaikum warahamatullah wabarakatuhu.
Bayani Akan cryptocurrency.
Crypto currency Wata fasahace da aka Dorata Akan Blockchain technology.
Blockchain technology wata fasahace da aka Dorata Akan internet wada Ake kirkirar fahasar robots da artificial intelligence, wato naurori masu sarrafa Kansu Akan Blockchain. AI Kamar chatgpt da grok da Kuma cryptographic.
Cryptocurrency, wani nauyin kudi ne KO kadara da Aka kirkira Akan Blockchain Wanda ya bambamta da fiat currency, Wanda yakasance a matsayin Digital currency.
Cryptocurrency zaman Kansa yakeyi ba tare da central control ba wannan dalilin ne yasa Ake Kiran crypto da decentralised wato babu wani Wanda yake control dinsa zaman Kansa yakeyi bakamar fiat currency 💵 ba Wanda dole akwai central bank da take regulating da controlling na kudi.
Cryptocurrency ya bambamta da fiat currency 💵 ta hantoyi da yawa Kamar haka.
Fiat currency idan kana da matsala sai kaje banki.
Idan zaka cire kudi masu yawa sai Ka cika wasu kaidoji.
Weekend KO public holiday Banki Baya aiki, da makamantan su.
Cryptocurrency ba ruwansa da Banki, Kuma zaka iya cire asset naka Komai yawansa Ka Kai inda kake so a kowane lokaci, Koda kuwa weekend ne KO public holiday crypto ba ruwansa da wannnan.
Cryptocurrency, Kai Kake da wuka da nama Akan asset naka zaka iya yin Yadda kake so a duk lokacin da Kaga dama.
Wani Mutum da Ake Kira da Satoshi Nakomoto Wanda Dan asalin Kasar Japan ne mazaunin America shine mutumin daya Fara kirkirar coins na farko a shekar 2009 Wanda Ake Kira da Suna Bitcoin.
A cryptocurrency akwai coins KO token.
Coins shine Kamar native currency na wani Blockchain kamar Ethereum, Solana, BNB da sauransu.
Token Kuma wani asset da aka dorashi Akan wani Blockchain kamar pancakeswap don yin amfani da network na wani Blockchain.
Akwai Stable coins Kamar USDT, USDC da sauransu wato su digital Dollar ne Wanda farashin su bazai wuce Dola 1 ba Komai dadewar da zaiyi.
Akwai normal coins Kamar Bitcoin, Ethereum , BNB da Solana. Wanda price dinsu ba stable bane missali Bitcoin anfara cinikayarsa a kasa da Dollar 1 a shekarar 2009 Aman Yanzu ana cinikayarsa Akan $125000 duk guda Daya Kuma ana SA ran zai Kai Dollarb1,000,0000 nan da shekaru 2.
Akwai jinsin coins Wanda Ake Kira meme coins Wanda Sukuma ana kirkirar su ne don nishadi, a social media Kamar su Shiba inu, Pepe, da sauransu.
Cinikayyar cryptocurrency abune mai hadarin gaske musamman idan coins din baida foundation Mai kyau.
Ana iya gane coins mai kyau Wanda idan akayi hakuri za a samu alkhairi ta hanyar technical analysis da fundamental analysis.
Ana cinikayar crypto ta hanyar scalping wato trading na Yan awowi, kwanaki, sati KO wata.
Akwai spot trading Wanda akeyi kulum Wanda shine trading da Malaman Addinin Musulunci suka bada fatawa Akan halaccinsa.
akwai feature trading, perpetual, rebet Wanda Yana da hadari sosai Kuma malaman Musulunci sun bada fatawa cewa feature, perpetual da reber trading haramun ne don haka Bai kamata Musulmi yayi ba.
Ana iya cinikayyar cryptocurrency ta hanyar saye don ayi holding zuwa wani lokaci Kamar shekara 5-10 hakan nada matukar faida sosai.
Ana cinikayyar cryptocurrency A Kasuwancin wato Decentralised exchange (DEX) Kamar Uniswap, pancakeswap, poocoin pump.fun da sauransu da Kuma centralised exchange (CEX) Kamar su Binance, kucoin, bitget, Bybit da sauransu.
Zaka iya staking/deligating na coin naka don samun riba wato Kamar Ka bada ajyar coins naka don samun lada kuma zaka iya ustaking/undeligating na coins naka duk lokacin da Kaga dama.
Akwai staking Fix Wanda Kai zaka zabi lokacin da kakeso Kamar wata, shekara da sauransu a irin wannan staking din baza Ka iya unstaking/undeligating na coins naka ba har sai lokacin da Ka zaba ya cika.
Akwai Kuma flexible staking Wanda zaka iya cirewa duk lokacin da Kaga dama.
Kadan Daga coins da zaka iya staking. Sune Kamar haka.
Ethereum, sui, core da sauransu.
Mutanen da sukasai bitcoin a kasa da Dollar daya daga shear 2011 zuwa 2025 cikin sheru 14 sune masu kudin Duniya a yanzu.
Ana iya gane darajar coins ta hanyar sanin Total supply wato yawansa, utilities da aka Gina akansa, liquidity kwato kudin da aka Dorata Akansa don yin cinikayya da Kuma use case.
Idan coins baida utilities masu yawa, KO karanci liquidity Kuma baida use cases sayen SA babban hadari ne.
Idan total supply na coins yazama Mai yawa sosai Kuma baida liquidity Mai yawa hakan zai iya kawo wa coins din cikas a kasuwa . Koda Yana da utilities da uses cases farashinsa bazai riqa saurin hauhawaba.
Comments
Post a Comment
Mun gode