ABUN DA YA KAMATA KASANI AKAN CORE
Menene Core DAO, kuma me ya sa yake da muhimmanci a duniyar Web3? A cikin duniyar Blockchain da Web3, akwai ayyuka da dama da ke kokarin haɗa tsaro, decentralization da amfani da Bitcoin tare da damar DeFi. Ɗaya daga cikin waɗannan ayyukan shi ne Core DAO, wanda token ɗinsa shi ne $CORE. Menene Core DAO? Core DAO wata blockchain ce ta Layer-1 da aka tsara domin haɗa wasu daga cikin manyan abubuwan da Bitcoin ya shahara da su—musamman tsaro da decentralization—da kuma damar amfani da smart contracts da DeFi. Manufar Core ita ce samar da yanayi inda masu amfani da Bitcoin da sauran cryptocurrencies za su iya shiga sabbin ayyukan Web3 ba tare da barin muhimman ka'idojin decentralization ba. Menene $CORE? $CORE shi ne native token na Core blockchain. Ana amfani da shi wajen ayyuka daban-daban a cikin ecosystem ɗin Core. Wasu daga cikin amfaninsa sun haɗa da: Biyan kuɗin transaction a kan network. Staking, inda masu amfani za su iya kulle $CORE domin taimakawa wajen tsaron ...